Rahotanni sun nuna cewa, shugaba Mansour ya nada shugaban gungun kawancen jam'iyyun adawar kasar ko "kungiyar fafitikar 'yantar da al'umma " kuma tsohon babban darektan hukumar makamashin nukiliya ta duniya, Mohamed El-Baradei a matsayin mataimakin shugaban gwamnatin wucin gadin kasar ne, don ya kula da harkokin kasashen waje, a hannu guda kuma, aka nada Hazem el-Beblawi a matsayin firaministan wucin gadi, don ya kafa gwamnatin wucin gadin kasar. Tuni dai Beblawi ya kama aikin zaben jami'an gwamnatin wucin gadi.
Jim kadan da sanar da nadin jami'an biyu, ministan kula da harkokin tsaron kasar Abdel Fattah al-Sisi, ya ba da jawabi ta gidan talabijin na kasar ta Masar, inda ya yi gargadi da a kauracewa dukkan abubuwan daka iya kawowa yunkurin kafuwar gwamnatin wucin gadin kasar illa. (Maryam)