Kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA, ya ba da rahoton cewa, kotun kasar Masar ta kebe ranar 25 ga watan Agusta, a matsayin ranar da za a tuhumi jagoran jam'iyyar 'yan uwa musulmi(MB) da mataimakansa guda biyu da wasu mambobin jam'iyyar, bisa laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa.
A cewar rahoton, laifukan da ake tuhumar tasu da aikatawa, sun hada da kashe jama'a, iza wutar tashin hankali kan masu bore da mallakar abubuwan fashewa da makamai ba bisa ka'ida ba.
Har yanzu dai, babban jagoran jam'iyyar Mohamed Badie na boye, amma ana tsare da mataimakansa guda biyu wato Khairat al-Shater da Rashad Bayoumi.
Ana zargin manyan jagororin jam'iyyar ta 'yan uwa musulmi da tunzura masu bore su yi tashin hankali a kusa da hedkwatar jam'iyyar a gundumar Moqattam da ke birnin Alkahira yayin boren ranar 30 ga watan Yuni wanda ya yi sanadiyar hambarar da shugaba Mohamed Morsi.(Ibrahim)