Ran 11 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya tattauna tare da ministan harkokin wajen kasar Masar Ahmed Mohamed Amr Darrag ta wayar tarho, inda ya nuna damuwarsa kan umurnin da gwamnatin kasar Masar ta bayar na cafko shugabannin kungiyar 'yan uwa musulmi, ya kuma yi kira ga jam'iyyu daban daban na kasar Masar da su yi shawarwarin zaman lafiya a tsakaninsu don warware matsalolin da ake fama da su a kasar.
Ran 11 ga wata, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana a birnin Moscow cewa, ya kamata a fara yin shawarwari tsakanin duk al'ummomin kasar da suke harkokin siyasa, zaman takewar al'umma da kuma addini, ta yadda al'ummomin kasar su da kansu su juya akalarsu.
Ran 11 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius shi ma ya yi kira da a kawo karshen rikice-rikice a kasar Masar don a fara ayyukan zabe na dimokuradiyya ta hanyar hada kan dukkan bangarorin da ke harkokin siyasa. Kasar Faransa na son ba da taimako ga Masar domin a samu yin sulhu a kasar. (Maryam)