Firaministan kasar Hazem Beblawi ne ya jagoranci sabbin ministocin, baya ga mataimakansa guda 3 da aka nada.
An rage yawan ministocin kasar cikin sabuwar gwamnatin wucin gadin daga 35 zuwa 33 dake cikin tsohuwar gwamnatin data shude, kuma tsohon ministoci a kalla guda 5 ciki har da ministan kula da harkokin cikin gida na kasar, na cikin wadanda za su ci gaba da ayyukansu a sabuwar gwamnatin. Bugu da kari, an yi kwaskwarima kadan kan wannan sabuwar gwamnati, ciki hadda kafa wata sabuwar ma'aikata ta lura da dokoki da sulhu yayin wannan lokaci na wucin gadi.
A wannan rana kuma, mai ba da shawara ga shugaban wucin gadin kasar Masar Adly Mansour ya bayyana cewa, fadar shugaban kasar ta riga ta fara yin tattaunawa tare da jam'iyyar 'yan uwa musulmi da dai sauran jam'iyyu daban daban don shirya taron neman sulhun duk fadin kasar, kuma galibin jam'iyyun musulmi za su halarci taron. Bugu da kari, a nan gaba, za a samu ministoci daga jam'iyyar Salafist Nour da jam'iyyar 'yanci da adalci ta 'yan uwa musulmi cikin gwamnatin kasar.
Ran 16 ga wata, wani mamban hukumar gudanarwar jam'iyyar 'yan uwa musulmi Mohamed Jamal Heshmat ya nuna cewa, jam'iyyar ba za ta halarci taron ba sabo da ba a kafa gwamnatin wucin gadin nan bisa dokoki ba. Kuma ba za a iya samu sulhu na gaskiya a kasar ba sai a maido da ikon Mohamed Morsi. (Maryam)