Shugaban rikon kwarya na Masar ya amince da kundin tsarin mulkin gwamnatin wucin gadin
A ranar Litinin ne kamfanin dillancin labarai na kasar Masar MENA, ya ba da labarin cewa, shugaban rikon kwarya na kasar ta Masar, Adli Mansour ya amince da kundin tsarin mulkin gwamnatin wucin gadin, bayan hambarar da Mohammed Morsi,
A cikin tanade-tanaden dokokin, har da jadawalin mika mulki ga gwamntain farar hula, kuma dokar za ta kare ne bayan an gudanar da zaben shugaban kasa, wanda aka shirya gudanarwa a farkon shekara mai zuwa. (Ibrahim)