in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa ne za a samu ci gaba cikin zaman lafiya a Zimabwe bayan babban zaben kasar
2013-08-06 16:55:25 cri
Kwanan baya, aka kammala zaben shugaban kasa, 'yan majalisar dokoki, da na kananan hukumomi a kasar Zimbabwe, shugaba mai ci yanzu, Robert Mugabe ya samu kuri'un da yawansu ya kai kashi 61.09 cikin 100, inda ya lashe mukamin shugabancin kasar a karo na 6, haka kuma jam'iyyarsa ta ZANU-PF ta samu kujerun da yawansu ya kai kashi 2 cikin 3 a majalisar dokokin kasar. Haka kuma, tawagar sa ido game da zabe ta kungiyar AU, da kungiyar raya kudancin kasashen Afrika SADC da ta kasar Sin sun amince da sakamakon zaben, amma kasashen yammacin duniya kamarsu Amurka da Australiya da sauransu sun bayyana cewa, an tabka magudi a zaben, inda suka nuna shakku game da sakamakon zaben, kana suka bukaci a sake shirya zabe a kasar.

Bisa ga halin da ake ciki yanzu, ba za a yi yiwuwar sake shirya zabe a kasar Zimbabwe ba. Sabo da na farko shi ne, tawagar sa ido game da babban zaben kasar Zimbabwe ta kungiyar AU, kungiyar SADC da ta kasar Sin sun amince da sakamakon zaben, kuma sun bayyana cewa, an shirya zabe cikin adalci kuma a bayyane, kuma sakamakon zabe ya nuna zabin jama'ar kasar. Sabo da haka ne, sun bukaci bangarorin da abin ya shafa na kasar da su amince da sakamakon zaben, haka kuma sakatare janar na M.D.D. Ban Ki-moon shi ma ya ba da wata sanarwa, inda ya jaddada cewa, yana fatan bangarorin da abin ya shafa za su girmama aniyar jama'ar kasar, game da sakamakon zabe, za su iya bayyana ra'ayoyinsu bisa hanyar da ta dace, sannan kuma za a saurari kukansu cikin adalci kuma a bayyane, wato ke nan, shi ma ya bukaci bangarorin da abin ya shafa da su amince da sakamakon zaben, da warware batun rarrabuwar kawuna da aka samu sakamakon babban zaben kasar cikin zaman lafiya.

Na biyu kuma, babban zaben kasar Zimbabwe, batun harkokin cikin gida na kasar, sauran kasashe ba su da ikon tsoma baki game da batun. Daga yadda shugaba Mugabe ke daidaita batutuwan kasar, ba zai yi saranda game da matsin lambar da kasashen yammacin duniya suka nuna ba. Haka kuma, kasashen yammacin duniya sun yi barazanar cewa, idan ba a sake babban zaben kasar ba, za a sake yin la'akari game da kakaba takunkumi ga kasar Zimbabwe, game da wannan, shugaban Mugabe ba zai ji tsoron kome ba. A watan Yuni na bana, yayin da wannan jarumi mai fafutukar yaki da mulkin mallaka mai shekaru 89, ke zantawa da manema labaru daga kasar Afrika ta Kudu, ya bayyana cewa, zai shugabanci jama'ar kasar don ci gaba da fafutuka, har sai ya sanya kasashen yammacin duniya sun soke takunkumin da suka kakabawa Zimbabwe a yanzu.

Daga halin da ake ciki a birnin Harare, babban birnin kasar, ana bin oda da doka yadda ya kamata, ba a samu wani tashin hankali bayan babban zaben ba. Daga ranar 2 ga wata wato daidai lokacin da aka bayar da sakamakon zabe, bangaren 'yan sanda ya fara jibge jami'am tsaro a kasar, don fuskantar rikicin da zai iya bullowa. Haka kuma, babban abokin hamayyarsa, wato tsohon firaministan gwamnatin hadaka ta kasar Morgan Tsvangirai, shi ma a madadin jam'iyyar MDC, ya ba da wata sanarwa, inda ya ce, zai dauki matakai cikin ruwan sanyi bisa doka, don warware rikicin zabe. Haka kuma, dukkan matakan da aka dauka ya ba da tabbaci cewa, ba za a sake samun rikicin zub da jini tamkar na shekarar 2008 a Zimbabwe ba, ana sa ran cewa, sabuwar gwamnatin Zimbabwe za ta samu ci gaba cikin zaman lafiya.

Bayan babban zaben kasar, ana sa ran kasar ta Zimbabwe za ta samu wani lokacin gaggauta farfado da tattalin arzikinta, da ma, Zimbabwe tana da masana'antu da aikin gona mai kyau, haka kuma, yawan jama'ar kasar da suka iya karatu da rubutu ya kai kashi 92 cikin 100, idan aka samu zaman lafiya, Zimbabwe za ta samu lokacin gaggauta bunkasuwar tattalin arzikinta cikin hanzari.

A cikin 'yan shekarun nan, duk da cewa, kasashen yammacin duniya sun ci gaba da kakaba mata takunkumi, nasarorin da ta samu sun kasance abin al'ajabi ga kasashen yammacin duniya, daga shekarar 2009 zuwa shekarar 2011, matsakaicin karuwar tattalin arziki na kasar ya kai kashi 9.4 cikin 100, a shekarar 2012, sabo da bala'in fari, wannan adadi ya ragu zuwa kashi 4 cikin 100, amma an yi hasashe cewa, yawan karuwar tattalin arzikin kasar bana, zai ci gaba da karuwa zuwa sama da kashi 5 cikin 100. Manazarta sun bayyana cewa, ainihin dalilin da ya sa, tattalin arzikin Zimbabwe ya samu farfadowa, shi ne, sabo da shugaba Mugabe ya dauki manufar "Looking East", wato ba wai Zimbabwe za ta ci gaba da dogora ga goyon baya daga kasashen yammacin duniya ba, kawai za ta karkata hankalinta ga kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki ciki har da kasar Sin. Haka kuma, a cikin shekarun nan, masana'antun kasar Sin sun ba da babbar gudummawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar. Sabo da haka, kafofin yada labaru suka bayyana cewa, bayan da shugaban Mugabe ya yi tazarce, tabbas ne zai ci gaba da gudanar da manufarsa, sabo da haka ne, zai ci gaba da kawo kyakkyawan yanayi ga kamfanonin Asiya ciki har da Sin don su je su saka jari a kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China