Hua ta fadi hakan ne yayin da take amsa tambaya dangane da matsayar Sin game da babban zaben kasar Zimbabwe da aka yi ranar Laraba.
Ta ce gwamnatin kasar Sin ta tura tawagar masu sa ido karkashin jagorancin tsohon jakadan Sin kan harkokin Afirka, Liu Guijin.
Tawagar ta baiyana cewa an yi zaben cikin lumana, natsuwa da kuma inganci kana an jefa kuri'a ba tare da tangarda ba cikin zamma.
Kasar Sin na taya kasar Zimbabwe murna dangane da nasarar gudanar da zaben, ta kuma kara da cewa Sin na mai nuna gamsuwa kan zammar 'yan kasar Zimbabwe game da kishin kasa da 'yanci.
Mai magana da yawun gwamnatin ta Sin ta yi kira ga al'ummar kasa da kasa su mutunta zabin mutanen kasar Zimbabwe.
Ta ce tana fata 'yan kasar Zimbabwe za su kuduri fara wani sabon shafin rayuwa a kasarsu cikin zaman lafiya, sulhu, bunkasa da kuma farfadowar kasar. (Lami Ali)