in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala babban zaben kasar Zimbabwe lami lafiya
2013-08-01 15:57:45 cri
Jama'ar kasar Zimbabwe sun dade suna saka ranar gudanar da manyan zabukan uku wato ran 31 ga watan Yuli. Ko da yake tun bayan da aka kafa hadaddiyar gwamnatin kasar Zimbabwe, aka daidaita matsalar hauhawar farashin kayayyaki, tare da samun farfadowar tattalin arziki a kai a kai, amma kafin hadakar, yadda gwamnatin ke gudanar da harkokin a kasar bai gamsar da mutanen ta ba. Don haka suna fatan babban zaben zai kawo karshen irin wannan yanayin da ake ciki, ta yadda za a samu makoma mai kyau a kasar a nan gaba.

Simon ya fara bin jerin masu kada kuri'a tun daga misalin karfe 8 na safe, gashi yanzu minti 40 ke nan ya wuce, duk da haka kuwa, yana farin ciki kwarai, ya ce,

"Wannan ne kasarmu, muna son jefa kuri'a, shi ya sa muna farin ciki sosai. Wannan ne ikonmu. Mu ne 'yan kasar Zimbabwe. Mun san mene muke yi."

Mutanen kasar Zimbabwe suna sa idon ganin wannan rana na gudanar da babban zabe sosai. hukumar zaben kasar Zimbabwe shi ma ya kammala shirin sa tsab don gudanar da wannan aiki. A sabili da haka, jama'a sun gamsu sosai kan yadda aka gudanar da zaben.

Bayan jefa kuri'a, mutane da yawa sun gaya mana cewa,

"An kada kuri'a lami lafiya, kuma yanayin da ake ciki a rumfunan jefa kuri'a ya yi kyau, an yi komai cikin tsanaki sosai."

"A ganina, an jefa kuri'a yadda ya kamata. Kuma a lokacin da ake bin layi kowa na ta hira da 'yan uwansa. Lallai yana da sha'awa sosai. Mutane suna kasancewa tare cikin lumana, hakan ya yi kyau!"

"Tsarin jefa kuri'a ya yi kyau! An gudanar da babban zaben yadda ya kamata."

A lokacin jefa kuri'a a wannan rana, mutane biyu sun jawo hankalin kowa da kowa, wato 'yan takara biyu masu karfi sosai, shugaba Robert Mugabe da firaminista Morgan Tsvangirai.

Mugabe wanda a lokacin da yaje kada kuri'an sa, ya nanata cewa, da zarar ya lashe zaben, zai dora muhimmanci kan bunkasa sinadaran ma'adinai, da raya aikin noma, da bunkasa tattalin arzikin kasar, a kokarin bude wani sabon babi na kasar Zimbabwe. Ya ce,

"Da zarar na lashe zaben, zan dauki nauyin bunkasa tattalin arzikin kasar bisa iyakacin kokarina, da daukar kwararran matakai domin bunkasa sinadaran ma'adinai da aikin noma."

A nasa bangare kuma, bayan kada nasa kuri'a, Morgan ya furta cewa,

"A matsayina wani dan Zimbabwe, ina fatan wannan babban zaben zai kawo karshen matsalar da kasar take fuskanta tun bayan shekarar 2008. Ina fatan kowa zai taimakawa kasar ta hanyar jefa kuri'a. Bayan da aka yi hamayya, da rashin amincewa da juna, yanzu na yi farin ciki kwarai da ganin cewa, mutane da yawa sun fito kada kuri'a, lallai hakan ya burge ni sosai. Yanzu Zimbabwe ta samu damar samun ci gaba."

An kai ga cimma shirin da aka tanada wajen kammala aikin kada kuri'un kafin karfe 7 na maraice na wannan rana. Kuma daga bisani an fara aikin kidayar kuri'u.

Shugaban tawagar sa ido kan babban zaben kasar Zimbabwe ta kungiyar AU, kana tsohon shugaban kasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya furta cewa,

"Kawo yanzu dai, kome na gudana lami lafiya, cikin lumana da kuma tsari. Wannan ne zaben da aka yi cikin 'yanci kuma a bayyane. Ba shakka sakamakon zaben zai nuna ra'ayin jama'ar kasar. Muna fatan kowa zai amince da wannan sakamako."

An yi kiyasin cewa, za a gabatar da sakamakon babban zaben kasar Zimbabwe cikin kwanaki biyar masu zuwa.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China