Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba da sanarwa a ranar Litinin cewa, ba ta da niyyar rushe kamfanonin jiragen sama da ba su girmama dokokin da suka shafi sufurin jiragen sama na fararen hula a cikin kasar. Darekta janar na hukumar kula da harkokin jiragen saman fararen hula ta Najeriya (NCAA), kaftan Fola Akinkuotu, ya yi wannan sanarwa a birnin Lagos, hedkwatar tattalin arzikin Najeriya.
Jami'in ya tunatarwa kamfanonin jiragen sama cewa, akwai dokokin dake daidaita wannan sana'a ta sufurin jiragen saman fararen hula, kuma ya zama wajibi a giramama wadannan dokoki.
Mista Akinkuotu ya bayyana cewa, hukumarsa za ta samarwa kamfanonin jiragen sama yanayi mai kyau da zai ba su damar gudanar da harkokinsu yadda ya kamata domin samun nasara, amma duk da haka, ya zama dole wadannan kamfanonin jiragen sama su girmama doka ta kowane hali. (Maman Ada)