Akalla firsinoni 175 ne suka tsere daga wani gidan yari dake garin Akure na jihar Ondo a tarayyar Nigeriya, bayan da wasu mahara da ba a san ko su waye ba suka kai hari gidan yarin ranar Lahadi 30 ga watan Yuni.
Wani babban jami'i a hukumar lura da gidajen yari Tunde Olayiwola ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua hakan, yana mai cewa, lamarin abu ne da ya baiwa kowa mamaki, kasancewar gidan yarin na makwaftaka da barikin sojoji dake yankin. Olayiwola ya tabbatar da cewa, za su yi iyakacin iyawarsu wajen tabbatar da hukunta masu hannu cikin aukuwar wannan laifi.
Shi ma a nasa bangare, kwamishinan 'yan sandan jihar Patrick Dokumor, wanda ya gane wa idanunsa halin da gidan yarin ke ciki, jim kadan da aukuwar lamarin, ya yi kira ga al'ummar jihar da su kwantar da hankalinsu, su kuma yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa, lamarin ba shi da alaka da ayyukan wasu 'yan ta'adda. Dokumor ya kuma tabbatar da cewa, tuni jami'an tsaro suka fara gudanar da bincike kan lamarin, za kuma su dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma. (Saminu)