Rundunar soji a Najeriya ta samu nasarar cafke wasu bata gari su 28, da ake zargi da fasa bututun mai a jihar Ogun dake kudu maso yammacin kasar.
Babban kwamandan bataliya ta 35, ta rundunar sojin kasar Birgediya Janar David Ahmadu ne ya tabbatar da hakan, yana mai cewa, an damke wadanda ake zargin ne yayin da suke tsaka da satar mai, daga bututun da suka fasa a yankin Ogere-remo dake jihar ta Ogun.
Ahmadu ya kara da cewa, wannan nasara ta cafke wadanda ya kira masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, ta biyo bayan bayanai da wasu al'ummar yankin suka baiwa rundunar tsaron dake kula da bututun man, mallakar kamfanin sarrafa albarkatun mai na kasar NNPC. Ana dai sa ran gurfanar da wadanda ake zargin gaban kuliya, da zarar an kammala bincike a kansu.
Najeriya ce kan gaba a dukkanin fadin nahiyar Afirka wajen haka da fidda danyan-mai, sai dai tana fuskantar kalubalen barnata bututun mai da bata gari ke yi, wadanda sau da dama ke fasawa, tare da dibar man daga bututun dake bi ta sassan kasar, duk kuwa da hadarin da hakan ke da shi ga rayuwarsu. (Saminu)