Tsohon firaministan mulkin wucin gadi na gwamnatin kasar Mali, Cheick Modibo Diarra ya ajiye takardar takaransa a ranar Litinin a zaben shugaban kasar Mali da za'a gudanar a ranar 28 ga watan Yuli mai zuwa, a cewar wata majiya ta kusa da tsohon faraministan.
Mista Diarra ya ajiye takardarsa ta takara a babban kotun tsarin mulki, a cewar na kusa da shi.
Mista Diarra shi ne shugaban jam'iyyar hada kan 'yan kasar Mali domin samun cigaba (RPDM), wanda da sunanta ya yi takarar zaben shugaban kasa na ranar 29 ga watan Afrilun shekarar 2012.
Bayan juyin mulkin sojoji na ranar 22 ga watan Maris na shekarar 2012, wannan ma'aikacin kasa da kasa, ya rike kujerar firaministan rikon kwarya kafin ya yi murabus dalilin matsin lamba daga sojojin da suka yi juyin mulki. (Maman Ada)