Kakakin MDD Martin Nesirky ya fada a ranar Litinin cewa, MDD za ta tura jirgin sama mai sarrafa kansa zuwa kasar jamhuriyar demokiradiyar Congo (DRC) saboda aikin wanzar da zaman lafiya, inda majalisar za ta kashe sama da dala miliyan 13 a ko wace shekara wajen kula da shi.
Nesirky ya shaidawa taron manema labarai cewa, ana sa ran tura jirgin ne a cikin 'yan makonni masu zuwa, kuma za a aiwatar da wannan shiri ne cikin shekaru 3, kana ana iya kara wani wa'adi na wasu shekaru biyu.
Kakakin na MDD ya ce, kamfanoni 25 daga kasashe 11 sun ziyarci kasar, domin su yi nazarin yankin tare da tawagar MDD da ke wurin, kana daga bisani wasu kamfanoni suka gabatar wa sashin kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD bukatar samar da jirgin.
Ya ce, sanar da wannan jirgi mai sarrafa kansa zai baiwa ma'aikatan wanzar da zaman lafiya damar sa-ido kan zirga-zirgar kungiyoyi masu dauke da makamai da kuma kare rayukan fararen hula yadda ya kamata, musamman a yankin da ke gabashin Afirka.
Nasirky ya kara da cewa, kamfanin da ya sarrafa jirgin ne zai rika kula da shi, karkashin tsauraran matakan tsaro na MDD, inda za a rika baiwa tawagar wanzar da zaman lafiyar da abin ya shafa bayanai da suka kamata wato MONUSCO da ke kasar da DRC. (Ibrahim)