Tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya da samar da daidaito a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC ko MONUSCO a takaice, ta bayyana damuwarta don gane da sake barkewar rikici a yankunan Kibati da Rusayo, dake da tazarar kimanin kilo mita 12 daga garin Goma dake gabashin kasar.
A cewar mataimakin kakakin babban magatakardar MDD Eduardo del Buey, fadan baya-bayan nan ya barke ne da sanyin safiyar ranar Litinin 20 ga watan nan da muke ciki, tsakanin dakarun rundunar sojin gwamnatin kasar da na 'yan tawayen kungiyar nan ta M23. An ce, yayin dauki ba dadin, bangarorin biyu sun yi amfani da manyan makamai da igwa-igwa domin kaiwa junansu hari.
Don gane da halin da ake ciki, rundunar ta MONUSCO ta ce, tana daukar matakan da suka dace, ciki hadda matakan diflomasiyya da na siyasa, domin kawo karshen halin zaman dar dar da ake ciki a kasar.
Shi dai wannan yanki na gabashin jamhuriyyar dimokaradiyyar Congo, na shan fama da rikice-rikice a wannan 'yan watanni, biyowa bayan daukar makamai da kungiyar 'yan tawayen M23 suka yi a Arewacin Kivu tun a farkon shekarar bara.(Saminu)