A ranar Laraba, magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya sanar da nada Abdallah Wafy, 'dan asalin kasar Nijar a matsayin mataimakin wakili na musamman a jamhuriyar demokradiyar Congo (DRC).
Wata sanarwa da mai magana da yawun magatakardan MDD ya bayar na mai nunin cewa, Wafy shi ne zai maye gurbin Leila Zerrougui, 'dan asalin kasar Aljeriya, inda zai jagoranci fannin kiyaye dokoki na cibiyar ta MDD wato a aikin kawo daidaito a jamhuriyar demokradiyyar Congo (MONUSCO).
Kafin a sanar da ba shi wannan mukami, Wafy yana aikin rikon mataimakin wakilin musamman na MDD tun watan Satumban shekarar 2012, kana shi ne kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban sashen 'yan sanda na MONUSCO, in ji sanarwar.
A makonni biyu da suka wuce, Mr. Ban ya bai wa Martin Kobler mukamin sabon wakili na musamman a kasar.
MONUSCO tana da dakaru da yawansu ya kai 17,000 kuma tana dauke da nauyin kare farar hula, kare hakkin bil adama dake cikin barazana ta zahiri, da kuma tallafawa ayyukan dakarun kasar ta Congo. (Lami)