A ranar Laraba, magatakardan MDD Ban Ki-Moon da shugaban babban bankin duniya Jim Yong Kim suka nuna goyon bayansu ga yunkurin kafa zaman lafiya na baya bayan nan a jamhuriyar demokradiyar Congo DRC, da ma a yankin baki daya.
Yayin ziyarar farko ta hadin gwiwa zuwa yankin tsakanin MDD da babban bankin duniyan, Kim ya sanar da samar da rancen dalar Amurka biliyan daya don taimakawa kasashe dake yankin Great Lakes, su samar da ababai kamar kiwon lafiya da ilimi, kara inganta harkokin cinikayya tsakaninsu, da kuma samar da kudin gudanar da ayyukan samar da wutar lantarki, duka da nufin tabbatar da ingancin yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla, in ji mataimakin mai magana da yawun MDD Eduardo del Buey, yayin jawabi ga manema labarai da aka saba yi.
Bayan wata ganawa da Joseph Kabila, shugaban kasar DRC da kuma ministocin gwamnati, Mr. Ban ya lura da cewa, wadannan kudade da za'a samar za su taimaka a fuskar aiwatar da harkokin zaman lafiya, tsaro da hadin kai a yankin.
Wannan ziyara wani yunkuri ne na nuna goyon baya ga yarjejeniyar zaman lafiya da MDD ta taimaka wajen kullawa, a watan Fabrairu tsakanin kasashe 11 da kungiyoyin kasa da kasa guda 4 (11+4) wacce ke da nufin kawo karshen tashin hankali da aka dade ana fama da shi da kuma fadace-fadace a DRC, domin a samu gina zaman lafiya a yankin.(Lami)