A ranar Alhamis ne mataimakiyar shugaban hukumar ayyukan bil adama na MDD Kyung-wha Kang ta kammala ziyarar aiki ta kwanaki hudu a jamhuriyar demokradiyyar Congo (DRC), bayan ta kai ziyara kauyen Mulamba dake kudancin yankin Kivu, in ji mataimakin mai magana da yawun MDD Eduardo del Buey, yayin jawabi ga 'yan jarida.
Del Buey ya ci gaba da cewa, yanzu haka wannan kauye ya zamo wajen zama ga dimbin jama'a da suka tsere saboda fadace-fadace a sauran sassan gabashin kasar Congo.
Ya ce, Miss Kang ta gana da al'umomi da suka rasa muhallinsu da kuma wadanda suka ba su mafaka, inda suka bayyana bukatar samar da kayan agaji, da ma tallafi na tsawon lokaci domin su samu sake ci gaba da rayuwarsu.
A lokacin ziyarar tata, ta je waje da hukumar abinci ta duniya karkashin MDD ke raba abinci, inda ta gane ma idonta yadda hukumomin MDD da ma sauran abokan hadin gwiwa ke kokarin isa wajen jama'a da kayayyakin tallafin ceton rai.(Lami)