Rundunar sojojin kasar demokaradiyar Congo FADRC da sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar (MONUSCO) sun kaddamar da wani aikin soja mai taken 'Strong Flank', a gundumar Arewacin Kivu domin gargadin 'yan tawayen M23 dake wajen Sake, in ji kanal Felix Basse, kakakin tawagar MONUSCO a yayin wani taron manema labarai na MDD da ya gudana a ranar 19 ga watan Yuni a birnin Kinshasa.
Ta hanyar wannan aikin soja na 'Strong Flank', sojoji da kwamandojin DRC sun bazu tare da sojojin MDD na MONUSCO a yankin Mugunga, domin gargadin duk wani motsi na 'yan tawayen M23 wajen Sake, daukar nauyin kiyaye tsaron fararen hula, da kuma tabbatar da ikon gwamnatin kasar a wannan yanki, in ji kanal Basse.
Sojojin MDD na kasar Tanzaniya da dakarun ko-ta-kwana na tawagar MONUSCO na cigaba da gudanar da sintiri sosai dare da rana a wannan yanki na Sake bisa hanyar zuwa birnin Goma, in ji wannan jami'i na MDD.
A cewarsa, a cikin tsarin ayyukan soja na hadin gwiwa na Forteresse Bleue na daya da na biyu, tawagar MONUSCO ta cigaba da ajiye sojojinta bisa tsaunukan gabashi da yammacin Munigi, domin kai taimakon da ya kamata ga sojojin FADRC dake kokarin tabbatar da zaman lafiya a Arewacin Kivu. (Maman Ada)