in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilan MDD sun yi kiran aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a DRC
2013-05-22 10:23:27 cri

A ranar Talata ne wakiliyar MDD a yankin Great Lakes na Afirka ta yi kiran a aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya a jamhuriyar demokradiyar Congo (DRC), tare kuma da nuna damuwa dangane da sake barkewar fadace-fadace a gabashin kasar.

Wakiliyar musamman ta magatakardar MDD a yankin Great Lakes na Afirka, Mary Robinson ta nuna damuwa matuka game da sake barkewar fada a wurare kusa da Goma, a gabashin kasar , in ji mai magana da yawun MDD Eduardo del Buey, yayin jawabi ga 'yan jarida a hedkwatar MDD a birnin New York.

Del Buey ya ci gaba da cewa, wakiliyar ta MDD ta yi kira ga bangarori da suka kulla yarjejeniya ta baya bayan nan da su kiyaye yarjejeniyar ta hanyar mai da hankali kan warware rikicin cikin lumana a gabashin kasar DRC da ma yankin baki daya.

A ranar Litinin, fada ya sake barkewa tsakanin 'yan tawayen kungiyar M23 da dakarun gwamnatin kasar Congo FARDC, a Kibati da Rusayo masu nisan kilomita 12 daga garin Goma, bisa rahoton da hukumar aikin kawo daidaito a DRC ta MDD, MONUSCO ta bayar.

Hukumar MONUSCO ta ci gaba da cewa, fada ya sake barkewa a Mutaho, mai nisan kilomita 12 daga Goma, kuma an shiga rana ta biyu, yayin da take kira a kara hakuri, a kuma ci gaba da kokarin ganin fadan bai yadu ba.

Yayin ziyararsa a kasar Mozanbique, magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya ce, fadan na baya bayan nan ya nuna muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar kafa zaman lafiya a DRC, da ma yankin Great Lakes baki daya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China