in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanar da tsawaita lokacin rufe ofisoshin jakadancinta a wasu kasashen waje
2013-08-05 15:16:17 cri
A ranar 4 ga wata, kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen Amurka Jennifer Rene Psaki ta sanar da cewa, Amurka za ta tsawaita lokacin rufe ofisoshin jakadancinta da ke kasashe 19 a yankin yammacin Asiya da nahiyar Afrika, don magance aukuwar hare-haren ta'addanci da za a samu.

Psaki ta ba da sanarwa game da wannan, inda ta ce, bayan da aka rufe su a makon da ya gabata, za a ci gaba da rufe wadannan ofisoshin jakadancin kasar Amurka a wadannan kasashe daga ranar 5 ga wata har zuwa ranar 10 ga wata, amma, daga ranar 5 ga wata, za a bude ofisoshin jakadancinta da ke kasashe 9, ciki har da kasashen Bangladesh, da Aljeriya, da Mauritaniya, Afghnistan, Iraqi da sauransu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China