in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta rufe ofisoshin jakadancinta da ke kasashen yankin Gabas ta tsakiya
2013-08-05 13:22:18 cri
A ranar 4 ga wata, Amurka ta rufe ofisoshin jakadancinta da ke kasashen Iraqi, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa da sauran kasashe 14 na wucin gadi, kuma mai yiwuwa ne, za a tsaiwaita lokacin rufe ofisoshin jakadancinta. Tuni gwamnatin Amurka ta bayyana cewa, dalilin da ya sa aka rufe wadannan ofisoshin jakadancin na da nasaba da batun tsaro

A wannan rana, yayin da wakilinmu ke zantawa da wani jami'in ofishin jakadancin Amurka da ke kasar Qatar, bai yi cikakken bayani ba, sai dai ya ce, ya zuwa yanzu, ba a tabbatar da lokacin sake bude ofishin jakadancin Amurka da ke Qatar ba.

Ofishin jakadancin Amurka da ke kasar Iraqi yana wata unguwa da ke babban birnin na kasar wato Bagadaza, don hana hare-haren ta'addanci da za a iya kai wa ofishin, a wannan rana, an kara inganta matakan tsaro a unguwar, inda jami'an tsaro suka yi unguwar tsinke, lamarin da ya yi sanadiyyar samun cunkoson motoci a cibiyar birnin na Bagadaza.

Har illa yau, kasashen Birtaniya da Amurka da Jamus da Faransa, sun rufe ofisoshin jakadancinsu a kasar Yemen, kuma a ranar 4 ga wata, kasar ta Yemen ta inganta harkokin tsaro a ofisoshin jakadancin wadannan kasashe 4, da hukumar M.D.D. da ke kasar, bisa labarin da aka samu, an ce, za a fara gudanar da ayyuka a wadannan ofisoshin jakadanci a ranar 6 ga wata.

Manazarta sun bayyana cewa, a 'yan kwanan baya, wasu fursononi sun tsere daga gidan yarin kasar Iraqi, kuma ba da dadewa ba, watan Ramadan zai kare, ana ganiu akwai yiwuwar masu tsattsauran ra'ayi na iya kara daukar makamai, hakan ne babban dalilin da ya sa Amurka ta rufe ofisoshin jakadancinta da ke kasashen Gabas ta tsakiya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China