Gidan talabijin din CNN ya ambato jami'an Amurka da suke da masaniya kan lamarin da cewa, sakamakon gabatowar karshen Ramadan, 'yan kungiyar Al-Qaida da ke Yemen suna gaggauta kulla makarkashiyar kai hari kan mutanen Amurka da na kasashen yammacin duniya, musamman ma wadanda suke kaiwa da kawowa a Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka. Daga ranakun 3 zuwa 6 ga watan da muka ciki, ofishin jakadancin Amurka da ke kasar ta Yemen ya fi fuskantar hadari, musamman ma a ranar 4 ga wata, inda kila a wannan rana ce 'yan ta'adda za su kai hari.
Jami'an sun kara da cewa, in halin da ake ciki bai canza ba bayan ranar 4 ga wata, to, kila za a ci gaba da rufe wasu ofisoshin jakadancin Amurka da ke kasashen waje. (Tasallah)