in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin DRC ta tabbatarwa fararen hula na Arewacin Kivu na kara ba da hadin kai tare da MONUSCO
2013-08-05 13:43:19 cri

Gwamnati za ta yi aiki tukuru tare da tawagar tabbatar da zaman lafiya ta MDD dake kasar DRC-Congo (MONUSCO) da kuma gungun kai daukin gaggawa na maido da zaman lafiya dake Arewacin Kivu, a cewar wata sanarwa da ta fito a ranar Lahadi a birnin Kinshasa daga bakin ministan sadarwa na kasar kuma kakakin gwamnati, mista Lambert Mende.

Mista Mende dake mai da martani kan wa'adin da fararen hular yankin Arewacin Kivu suka gabatarwa gungun kai daukin gaggawa na maido da zaman lafiya na MDD dake Arewacin Kivu domin farautar kungiyoyin dake dauke da makamai, ya bukaci jama'ar yankin da su baiwa gwamnatin kasar yardarsu, ta yadda za ta aiki tare da tawagar MONUSCO tare kuma da cewa, wannan aiki zai iyar daukar lokaci.

Haka kuma mista Mende ya nuna takaicinsa na cewa, bai kamata ba wasu jama'a masu zaman kansu su baiwa wata kungiyar kasa da kasa wani wa'adi ba. 'Mun yi imani da halin da suke ciki da bacin ransu game da tashe-tashen hankalin da suke fama da su a bainar idon duniya.' in ji mista Mende.

Jami'in ya bayyana cewa, gwamnati ita ma tana damuwa da wannan hali kamar saura, amma kuma tana bin wannan matsala sannu a hankali ta yadda za ta daidaita ta.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar daya ga watan Agusta ne, fararen hula na Arewacin Kivu suka ba da mako guda ga sojojin MDD domin su fara kai samame, idan ba haka ba, jama'ar wurin za su janye goyon bayansu ga gwamnatin kasar da tawagar MONUSCO. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China