in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummomin Arewacin Kivu a DRC suna goyon bayan ra'ayin shugaban Tanzania
2013-06-28 10:51:55 cri

Al'ummomin gudumar Arewacin Kivu dake gabashin DRC-Kinshasa sun bayyana goyon bayansu kan ra'ayin shugaban kasar Tanzania Jakaya Kikwete domin ganin kasashen Rwanda da Uganda su yi shawarwari tare da 'yan tawayen dake cikin kasar DRC, a cewar wata budadiyar wasika da wadannan al'ummomi suka aikawa MDD.

Ya kamata gamayyar kasa da kasa ta yi matsin lamba domin wadannan kasashe su bude hanyar shawarwari ba tare da bata lokaci ba, tare da 'yan tawaye da amsa bukatun demokaradiya kamar sauran kasashe da ma kasar DRC, in ji wannan takarda.

Wannan hanyar neman sulhu tana da alfanu fiye da saura, domin tana janye wa kasashen Rwanda da Uganda dalilin da suke amfani da shi wajen kawo zaman dar dar a kasar DRC, in ji Jean Sekabuhoro, shugaban jituwar al'ummomin Arewacin Kivu, tare da kara bayyana cewa, kasashen Rwanda da Uganda ba za su kiyaye tsaronsu ba ta hanyar janyo rashin tsaro a kasar DRC. A cewarsa, kasar DRC na da fiye da miliyan daya na 'yan gudun hijira da wadanda suka kaura domin wadannan kasashe biyu na ganin cewa, farautar 'yan tawaye har cikin DRC, na ba su damar kare kansu da kansu.

Shugaban kasar Tanzania, Jakaya Kikwete ya gabatar da ra'ayin nasa ne a yayin bikin cikon shekaru 50 da kafuwar kungiyar AU. Tanzania na daga cikin kasashe uku da suka ba da sojoji domin kafa rudunar kiyaye zaman lafiya ta MDD, dake da nauyin karbe makamai da farautar gungun kungiyoyin 'yan tawayen dake gabashin DRC.

Kungiyar 'yan tawayen FDLR ta kasar Rwanda da hadin gwiwar kungiyoyin 'yan tawayen ADF da na NALU na kasar Uganda na cigaba da ayyukansu a gabashin DRC cikin shekaru da dama. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China