Fiye da fursunoni 240 ne suka ari ta kare daga gidan yarin Kangwaye dake birnin Beni na jihar Arewacin Kivu na kasar DRC-Kinshasa, in ji wata majiyar da ta sheda yadda lamarin ya faru da ta bukaci a sakaya sunanta a wata hirar kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Wani mauzanin Beni ya bayyana cewa, an kai wannan hari da misalin karfe hudu na safe agogon wurin. Bisa fursunoni 339, 245 sun samu nasarar tserewa, jami'an tsaro dake wurin sun kashe fursuna guda, haka kuma an yi asarar kadarori masu tarin yawa, a cewar wannan majiya.
Yan sanda da jami'an tsaro dake gadin gidan yarin na Kangwayi sun bayyana cewa, abin ya fi karfinsu gaban makaman da wadannan mutane suka yi amfani da su wajen kai harin.
Wannan hari na gidan yarin Kangwayi, ana masa shedar hannun mutanen gungun 'yan tawayen Mai Mai da ba'a tabbatar da asalinsu da suka fito daga yankin Bashu bayan sun ratso ta Kalau ko kuma Nyaleke, in ji wata kungiyar farar hula dake Arewacin Kivu. (Maman Ada)