Rahotanni daga hedkwatar kungiyar EU na bayyana cewa, zaman majalissar zartaswar kungiyar don gane da harkokin kasa da kasa, ya amince da dage takunkumi kan shigar da makaman kare kai zuwa kasar Sham.
Wata sanarwar bayan taron na ranar Litinin 27 ga wata ta ce, majalissar zartaswar ta amince da batun tabbatar da takunkumi ga kasar ta Sham a sauran fannoni, in ban da bangaren makamai, da ragowar kayan aikin kare kai, da za a baiwa gamayyar kungiyar 'yan adawar kasar damar mallaka, domin kare fararen hula daga hare-haren da dakarun gwamnati ke aiwatarwa. Sanarwar ta ce, ana sa ran fara aiwatar da wannan kudiri ne tun daga farkon watan Agusta mai zuwa, za kuma a shafe shekara guda ana gudanar da shi.
Har ila yau ana sa ran daukar matakan tabbatar da cewa, kayayyakin da za a ba da damar shigar wa kasar, ba su fada hannun tsagin gwamnatin shugaba Bashar Al-Assad ba. Sanarwar ta kuma ce, ban da batun dage takunkumi kan makamai, za a ci gaba da aiwatar da ragowar kudurori da suka hada da na takunkumi kan hada-hadar kudade, da na ayyukan raya kasa, da ma batun tattalin arziki da rufe asusun ajiyar gwamnati.
Matakin kakabawa gwamnatin Sham takunkumi dai ya biyo bayan kokarin karya lagon 'yan adawa da gwamnatin kasar ta Sham ta fara tun tsakiyar watan Maris na shekarar 2011, matakin da kungiyar ta EU ta ce, ya saba wa dokokin kare hakkin bil-adama.(Saminu)