in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Masar sun gargadi magoya bayan Morsi da su guji tunzura jama'a da makamai
2013-07-09 13:50:56 cri

Sojojin kasar Masar sun fada a ranar Litinin cewa, kashe mutane a wajen hedkwatar jami'an tsaro na musamman da ke Alkahira, ya faru ne sakamakon tunzura sojojin da magoya bayan Mohammed Morsi suka yi, inda suka kai hari kan harabar hedkwatar sojojin da harsasai na zahiri.

Kakakin dakarun Masar kanar Ahmed Mohamed Ali, ya shaidawa wani taron manema labari na hadin gwiwa da kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar cewa, sun fatattaki masu boren ne da suka yi cincirundo a harabar jami'an tsaro na musamman, yayin da suke amfani da harsasai na zahiri, duwatsu, da sauran makamai kan dakarun.

Wani jami'in ma'aikatar lafiya ta kasar ya bayyana cewa, yawan wadanda suka mutu a fadan na ranar Litinin tsakanin dakarun tsaro da magoya bayan shugaban da sojoji suka tumbuke, ya karu zuwa 51, yayin da 435 suka jikkata sakamakon harbin bindiga.

Don haka, sojojin na Masar ke yin kira ga dukkan masu zanga-zanga da su bar dandalin taron jama'a, suna masu alkawarin cewa, ba za a hukunta su ba.  (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China