in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai wa sansanin sojojin Amurka hari da ke Afghanistan
2012-12-03 11:16:24 cri
A ran 2 ga watan Disamba, an kai wa wani sansanin sojojin sama na hadin gwiwa tsakanin kasashen Amurka da Afghanistan da ke birnin Jalalabad a gabashin kasar ta Afghanistan harin kunar bakin wake na bam wanda ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutanen Afghanistan guda 5 tare da jikkata sojojin NATO da dama.

A cikin wannan rana da safe, wajen karfe 6, 'yan kunar bakin waken sun tuka motoci biyu da aka dasa bama bamai cikin sansanin cikin sauri, daga baya, an samu musayar wuta tsakanin bangarori biyu ta kusan awoyi biyu. Kungiyar Taliban ta dauki alhakin wannan hari, wanda ya kasance hari mafi girma a cikin hare-haren da suka faru a sansanin sojojin saman da ke birnin Jalalabad tun watan Fabrairu na shekatar bana.

Hukumar 'yan sanda kasar Afghanistan ta bayyana cewa, dakaru 9 ne suka kai wannan hari, 3 daga cikinsu sun mutu sakamakon fashewar bam, a yayin 6 suka mutu a cikin musayar wuta. Bangaren NATO ya dauka cewa, masu kai harin ba su cimma burinsu ba saboda ba wanda da ya kai harin ya shiga babbar kofar sansanin. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China