in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kafa wani sansanin kera motocin injuna a kasar Habasha
2011-12-20 16:11:10 cri

Ranar Litinin 19 ga wata a nan birnin Beijing, kamfanin CSR na kudancin kasar Sin ya sanar da cewa, zai kafa wani sansanin kera motocin injuna a kasar Habasha tare da gabatarwa kasar fasahar kera motocin injuna na lantarki.

A cikin wannan shekara, yawan kudin da kamfanin ya samu a kasashen waje ya karu da kashi 200 bisa 100 ko fiye,sannan kayayyakin da ya fitar sun shafi kasashe da yankuna fiye da 60 a nahiyar Asiya, Turai da Afrika. Har ila yau kamfanin a cikin wannan shekarar ya sa hannu kan kwangilar tsawaita lokacin tabbatar da ingancin injunansa na tsawo shekaru 3 tare da kasar Sudan.

Darektan kamfanin CSR Zhao Xiaogang ya bayyana cewa, aikin fitar da kayayyaki masu amfani da fasahar zamani mai zurfi ya taimakawa kamfanin wajen samun bunkasuwa mai kyau a kasashen waje.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China