in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al-Qaida ta tabbatar da mutuwar manyan zaratanta biyu
2013-06-17 13:23:40 cri

Kungiyar Al-Qaida ta tabbatar da mutuwar manyan zaratanta biyu a fagen daga a arewacin kasar Mali wadanda suka hada da 'dan asalin kasar Aljeriya Abou Zeid da kuma 'dan asalin kasar Mauritaniya Abdallah Al Chinghtty da aka fi sani da Mohamed Lemine Ould Al Hacen, a cikin wata sanarwar da kamafinin dillancin labarai na Nouakchott (ANI) ya samu kofinta a ranar Lahadi.

A cewar wannan sanarwa, mutanen biyu dake jagorantar mayakan Katibas wato Alvourghan da Tarek Ibn Zeyad, an kashe su a lokacin bata kashin da ya hada kungiyar da sojojin kasar Faransa da na Chadi, yau da kusan 'yan watannin da suka gabata a lokacin da suke kokarin mamaye tsaunukan Tigharghart dake arewacin kasar Mali. Haka kuma wasu mayakan na kungiyar sun mutu a yayin wadannan yake-yake, in ji wannan sanarwa tare da jaddda cewa, harin da a cikinsa Abou Zeid ya mutu ya hadasa asarar rayukan abokan gaba da dama daga bangaren sojojin kasar Chadi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China