in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ta sake baiwa jami'an tsaro damar jefa kuri'a
2013-07-27 15:55:29 cri

A ranar Juma'a 26 ga wata, jami'an kasar Zimbabwe suka bayyana cewa, kotun tsarin mulkin kasa ta Zimbabwe ta yanke hukuncin ba da dama ga jami'an 'yan sanda da masu aikin zabe guda dubu 26,160 wadanda ba su samu damar jefa kuri'a kan babban zabe ba da a bar su su jefa tare da sauran jama'a a ranar 31 ga watan Yuli.

Jami'an ba su samu damar jefa kuri'a ba ne saboda matsaloli na kayan aiki da kuma jinkirin buga takardun jefa kuri'a.

Hukumar zabe ta kasar Zimbabwe ta gabatar da korafi a gaban kotu a ranar Talatar da ta gabata. Mataimakiyar shugaban hukumar zaben Joice Kazembe ta ce hukumar zaben ba ta son a hana wadannan jam'ai su jefa kuri'a saboda kalubale.

Ana sa ran cewa a ranar 31 ga watan Yuli 'yan kasar Zimbabwe za su yi zaben shugaban kasa, 'yan majalisu da shugabannin kananan hukumomi. Shugaba dake kan kujera a yanzu Robert Mugabe da Fraministan kasar Morgan Tsvangirai su ne manyan masu takarar kujerar shugaba kasar.(Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China