Shugaban kungiyar hadin-kan tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma a wannan zagaye wato ECOWAS, kana shugaban kasar Cote d'Ivoire Alssane Ouattara ne ya tabbatar da hakan a jiya Alhamis a birnin Abuja.
Yayin da yake zantawa da kafafen watsa labarai a wajen zaman taro karo na 43 na kungiyar ECOWAS a Abuja. Shugaba Ouattara ya ce ya samu wata wasika daga shugaban tarayyar Najeriya Dr. Goodluck Ebele Jonathan, cewa saboda la'akarin da yanayin tsaron da ake ciki a Najeriya, kasar na da bukatar ta dawo da wasu sojojinta daga Mali. Ouattara ya yi bayanin cewa, sai dai ba dukkan sojojinta za ta janye ba daga Mali,
Shi ma da yake karin haske game da hakan, darekatan watsa labarai na hukumar tsaro wato DDI Birgediya Janar Chris Olukolade ya ce za'a fara janye sojoji ne nan ba da dadewa ba, kuma za'a janye su ne bisa ka'idoji da MDD ta tanada.
Olukolade ya kara da cewa ba za'a janye jami'an tsaron gaba daya ba ko cikin gaggawa, amma dai za'a bi tsarin da ake bi na diflomasiyya don kada a haifar da sakaci wadda ka iya kawo sabon rikici nan gaba.
Janar Olukolade ya ce, kasar Najeriya, a hukumance, ta yanke shawarar bin ka'idojin da aka zartar na Majalisar Dinkin Duniya, kuma aka amince da shi a diflomasiyyance game da janye jami'an tsaro a duk inda ake tarzoma ko tashin hankali domin samun zaman lafiya mai dorewa kuma na dindindin. (Murtala Zhang)