Wannan jami'i ya bayyana cewa, za a jibge wadannan 'yan sanda a rumfunan kada kuri'a dake birnin Bamako, tare da yin rangadi a tituna daban daban, don shawo kan dukkan wata matsala da za ta taso a yayin jefa kuri'a.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a yankunan Kidal, Tambouctou, da kuma Gao dake arewacin kasar, sojojin Mali da hadaddiyar rundunar sojan kiyaye zaman lafiya ta MDD da kuma sojojin Faransa za su kiyaye tsaro a yayin babban zaben.
A ranar daya ga wata, tawagar musamman mai samun goyon baya daga kasashen duniya dake karkashin jagorancin kasashen nahiyar Afirka a Mali, ta mika nauyin ayyukan mulkinsa ga tawagar musamman kan batun Mali ta MDD a hukunce, inda hakan ya nuna cewa, MDD ta fara gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a Mali a hukunce. Babban aikin tawagar shi ne daukar nauyin tabbatar da tsaro a yayin babban zaben kasar da ma a yankunan arewacin kasar Mali.(Fatima)