Rahotannin da kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua ya fitar na nuna cewa, an bude runfunan zaben ne tun daga misalin karfe 8 na safe. Ana dai sa ran zaben kasar ta Mali zai kawo karshen rikicin siyasar da ya kici-yaki-cinyewa tun cikin watan Maris na shekarar bara, yayin da soji suka hambarar da zababbiyar gwamnatin kasar, yayin da kuma Arewacin kasar ya fada hannun 'yan tawayen kasar. (Saminu Alhassan)