in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ai fiye da dubu 5 ne za su sa ido kan zaban shugaban kasar Mali
2013-07-28 16:30:36 cri

Ranar 27 ga wata, kwamitin kula da harkokin zabe mai zaman kansa na kasar Mali ya bayyana cewa, wata tawagar da masu sa ido fiye da dubu 5 daga gida da wajen kasar ta Mali za ta sa ido kan yadda za a jefa kuri'ar zaben shugaban kasar a zagaye na farko.

Kwamitin ya ba da labarin cewa, a cikin wannan tawagar 'yan sa ido, akwai masu sa ido 3830 na kasar ta Mali da kuma wasu 1281 daga kasashen waje. Yawancin masu sa ido na kasar sun fito ne daga wasu kungiyoyi da hukumomi na kasar masu zaman kansu, yayin da na kasashen waje suke daga kungiyar tarayyar Afirka da ta Turai, kungiyar kasashe masu amfani da harshen Faransanci, kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS da dai sauransu.

Ban da haka kuma, kasashen Afirka ta Kudu, Nijeriya, Amurka su ma sun aika da nasu masu sa ido zuwa kasar ta Mali. An labarta cewa, za a aika da wadannan masu sa ido zuwa manyan yankuna guda 8 na kasar, inda za su sa ido kan yadda za a gudanar da babban zaben daga farko zuwa karshe.

Bisa shirin da aka tsara a baya, an ce, za a jefa kuri'ar zaben shugaban kasar ta Mali a zagaye na farko ranar Lahadin nan. Idan babu wanda ya sami rabin kuri'u ko fiye da haka, za a gudanar da zagaye na biyu na zaben a ran 11 ga wata mai zuwa. 'Yan takara 27 ne dai suka shiga zaben zama shugaban kasar a wannan karo, ciki had da tsoffin firaministocin kasar 4 da wasu 'yan siyasa masu fada-a-ji.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China