in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 6 sun halaka a wani harin bam
2013-07-30 15:33:28 cri
Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya aiko mana cewa hukumar 'yan sanda ta tabbatar da akalla mutane 6 ne suka halaka sannan wadansu suka ji rauni a jiya Litinin cikin wani harin bam da aka kai a garin Kano dake arewacin Nigeriya.

Fashewar har sau 3 sun auku ne a wata mashaya dake unguwar sabon gari, inda mafi yawan mazaunan wajen mabiya addinin Krista ne, jim kadan da kammala sallar isha'i, sannan daga baya aka rika jin karan harbe harben bindiga ta ko ina.

Kakakin rundunar tsaro ta hadin gwiwwa na JTF kaftin Ikedichi Iweha ya tabbatar da hakan amma bai yi wani Karin haske ba. Sai dai wani jam'in sojin da bai bayyana sunan sa ba ya ce ana kyautata zaton wadanda suka mutu sun kai 11. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China