in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda 4 a jihar Yobe
2013-04-12 16:57:36 cri
Ranar Alhamis 11 ga wata ne, wasu gungun 'yan bindiga suka kai hari kan wani ofishin 'yan sanda a Babangida dake karamar hukumar Tarmowa ta jihar Yobe, tarayyar Najeriya.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Yobe Alhaji Sanusi Rufa'i ya tabbatar da lamarin a Damaturu inda yace, akwai 'yan sanda guda hudu wadanda suka rasa rayukansu a musanyar wutar da suka yi da 'yan bindiga, yayin da 'yan bindiga guda biyar ne suka mutu.

Babangida dake karamar hukumar Tarmowa na da tazarar kilomita 50 arewa da birnin Damaturu.

Wadanda suka ganewa idanunsu faruwar lamarin sun fadawa kafafen watsa labarai cewa, 'yan bindigar sun bude wuta kan wannan ofishin 'yan sanda, inda suka gwabza kazamin fada tare da 'yan sanda har na tsawon awa guda, amma ba su kai hari kan fararen-hula dake garin Babangida ba.

Sanusi Rufa'i ya ce, ma'aikatan tsaro dake jihar Yobe za su ci gaba da kokarinsu, na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wurin, ta yadda mutanen da suke bin doka da oda za su gudanar da ayyukansu cikin yanayi mai kyau.

Jihar Yobe ta sha fama da hare-haren 'yan bindiga. Harin da aka yi ranar Alhamis din nan, ya faru ne kwanaki hudu bayan da aka yi dauki-ba-dadi tsakanin sojojin hukumar tsaro ta JTF da 'yan bindiga a kauyen Tumbulgi dake karamar hukumar Geidam na jihar, inda aka hallaka wasu sojoji gami da 'yan bindigar guda hudu.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China