Muhammadu Zakari,Shugaban daya daga cikin kananan hukumomin jihar ya sheda ma manema labarai a Jos babban birnin jihar cewa kauyawa 5 da daya daga cikin maharan ne aka kashe a kauyen sannan sauran maharan suma aka ji masu rauni.
Salisu Mustapha kakakin rundunar tsaron hadin gwiwwa shima ya tabbatar da faruwan wannan lamari,inda yayi bayanin cewa jami'an tsaron da suka yi sauri isa wajen ne suka samu nasarar harbe daya daga cikin maharani lokacin da ya nemi tserewa,kuma yanzu komai ya lafa a wannan wuri.
Har ila yau a wannan rana ta lahadin ne mahukuntar Soja suka tabbatar da cewa a kalla mutane 25 ne aka kashe a wassu harin daban daban a jihar Borno dake arewa masu gabashin kasar.
Haruna Mohammed Sani,kakakin rundunar tsaro na hadin gwiwwa ya yi bayanin cewa maharan da ake kyautata zaton kungiyar 'yan boko haram ne sun bude wuta a kan fararen hula da 'yan banga dake aiki a gundumar Dawashi na karamar hukumar Kukawa wanda ke kan iyaka da kasar Chadi.
haka kuma shima Kakakin rundunar tsaron hadin gwiwa na JTF Sagir Musa ya sanar da cewa an kashe mutane 5 a wani hari daban a Mainok nan kusa da garin Maiduguri babban birnin jihar.(Fatimah Jibril)