in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fuskanci fashewar abubuwa a arewacin Najeriya
2013-04-05 10:14:26 cri
Jami'an 'yan sanda sun bayyana cewa an fuskanci fashewar abubuwa a jihar Kano dake arewacin Najeriya, to amma babu wanda ya mutu ko kuma jikkata.

Wani bom ya fashe a rawul din Dangi dake hanyar zoo road, inda hakan ya janyo rudani matuka ga jama'ar unguwar. Jami'an binciken gano bom sun je inda bom din ya tashi.

Wakilin kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua dake jihar ya bayyana cewa jami'an binciko bom daga hukumar 'yan sanda sun gudanar da bincike a unguwar don tabbatar da cewa babu wani sauran bom irin wanda ake kirkirowa. Wakilin ya ci gaba da cewa an ji harbin bindiga bayan tashin bom din.

Jami'an tsaro suna unguwar kawanya yayin da mutane ke ta kansu don kare lafiyarsu.

Mazauna kusa da inda bom din ya tashi sun zauna cikin gidajensu don gudun kada tsautsayi ya hau kansu.

Mai magana da yawun hukumar tsaro ta JTF captain Ikedichi Iweha ya tabbatar da fashewar abubuwan, to amman ya kara da cewa babu wanda ya mutu ko samun rauni sakamakon hakan. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China