in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane hudu suka ji rauni sakamakon wani harin da aka kai a arewacin kasar Nijeriya
2013-03-13 10:05:40 cri

An ji karar bindigogi a wata makarantar firamare dake birnin Kano a arewacin kasar Nijeriya, lamarin da ya yi sanadiyar raunana wasu malaman makaranta hudu.

Kakakin 'yan sandan Kano Musa Majiya ya bayyana cewa, 'yan bindiga sun yi niyyar kai harin ne kan malaman wannan makaranta, inda suka tsare hudu daga cikinsu tare da yin harba bindigogi a gaban dalibai.

Ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan hari, amma an zargin kungiyar Boko Haram da hannu cikinsa, kungiya mai tsattsaurancin ra'ayin kishin islama mafi girma a kasar Nijeriya.

An ba da labari cewa, an rika samun hare-hare kwanan baya da ake dangantawa da wasu kungiyoyin kishin islama dake karkashin Boko Haram da suka rika garkuwa da mutane da kuma kai hare-hare. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China