Ranar Lahadin da ta gabata ne, shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana matukar takaici da bakin-ciki game da harin nan da aka kai kan 'yan makaranta dake kauyen Mamudo na jihar Yobe, kuma ya bayyana hakan a matsayin wani mummunan aiki.
Ta bakin mai baiwa shugaban kasar shawara na musamman ta fannin watsa labarai, Dr. Reuben Abati, Goodluck Jonathan ya ce babu wata barazana da zata karya lagon yunkurin da gwamnatinsa ke yi na samar da zaman lafiya a yankunan kasar baki daya.
A cewar shugaban Najeriya, duk wanda ya yi niyyar hallaka yaran da basu san hawa ba balle sauka, sakamakon zafin kai, hakika ba zai gama da duniya lafiya ba.
Har wa yau kuma, ya nuna jaje ga iyalan yaran da wannan mummunan hari ya shafa, yana mai ba da tabbacin cewa, gwamnatinsa zata kawo karshen ayyukan ta'addaci a kasar.(Murtala)