Wasu mahara su kimanin 8 sun kai farmaki wata unguwa mai suna Hausari, dake garin Maiduguri a Jihar Borno, a Arewa maso Gabashin Nijeriya, inda nan take suka hallaka kimanin mutane 19, ciki hadda mata 4, da kuma yara kanana 2.
Wasu rahotanni daga rundunar jami'an tsaro sun tabbatar da faruwar wannan lamari, sun kuma bayyana cewa, maharan da suka shiga wannan unguwa a ranar Juma'ar da ta gabata, sun boye makamansu ne cikin wata makara, domin yaudarar jami'an tsaron dake yankin. Har ila yau an ce maharan wadanda ake zaton 'yan kungiyar nan ta Boko Haram ne, sun kai farmakin ne unguwar ta Hausari, domin ramuwar gayya ga kame 'yan uwansu da 'yan kungiyar kato-da-goror yanki suka yi.
Wani mazaunin unguwar mai suna Ba'ana Ali, wanda ya gane wa idon sa faruwar lamarin, yace ba'a gane cewa wadannan mutane mahara ba ne, har sai da suka fara harbin kan-mai-uwa-da-wabi, kafin daga bisani a cewarsa sojoji su yiwa wurin tsinke, su kuma kame 6 daga cikinsu.(Saminu)