Rundunar jami'an tsaro ta hadin gwiwa a jihar Borno, dake arewa maso gabashin Najeriya, ta gano wani wagegen kabari, da wani rami na boye makamai da rundunar ke kyautata tsammanin magoya bayan kungiyar nan ta Boko Haram ne ke amfani da su a arewa maso gabashin birnin Maiduguri.
Da yake kewayawa da 'yan jaridu wadannan wurare a ranar Lahadi 14 ga watan nan, kakakin rundunar Laftana Kanal Sagir Musa yace, an gano tarin makamai, da kudi masu tarin yawa a wannan wuri. Musa ya kara da cewa, an gano wasu wuraren makamantan wadannan a unguwannin Aljajeri da Faluja dake cikin birnin Maiduguri, wuraren da acewarsa 'yan kungiyar ta Boko Haram ke amfani da su wajen binne mutanen gari, da kuma 'yan uwansu da aka kashe yayin dauki-ba-dadi da suke yi da jami'an tsaro.
Idan dai ba a manta ba, tsakanin ranar 3 zuwa 8 ga wannan nan na Yuli ne rundunar jami'an tsaro a jihar ta Borno, suka kai farmaki unguwannin Bulabulin Nganaram, da Aljajeri da kuma Faluja, lamarin da ya ba su zarafin korar magoya bayan kungiyar daga sansaninsu dake wadannan yankuna, tare da gano wasu ramuka na karkashin kasa, da suke amfani da su wajen boye makamai.
Har ila yau, samamen ya sabbaba kisan daya daga jagororin kungiyar da ake wa lakabi da jagoran yankin Bulabulin Nganaram, wanda ake zargi da kisan wani malami, da dalibai 3 a makarantar sakandaren Sanda-Karami, dake unguwar Ruwan Zafi a birnin na Maiduguri. (Saminu)