in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nigeriya sun ce ba a yi ma kowa barna ba a harin da ake yi ma 'yan ta'adda
2013-05-26 16:39:02 cri
Sojojin Nigeriya da yanzu haka suke farautar 'yan ta'adda a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar sun ce, ya zuwa yanzu babu wani abin da aka lalata a farautar da suke yi na 'yan ta'addan nan na Boko Haram.

Kakakin rundunar sojin tsaron na hadin gwiwwa Laftanar Kanar Sagir Musa a ganawar da ya yi da manema labarai a garin Maiduguri, ya yi bayanin cewa, ba'a kashe ko wane farar hula ba a wannan harin da ake yi ma 'yan ta'adda ta jiragen sama a sansanin 'yan kungiyar Boko Haram din da aka gano guda uku a wani gandun daji na Sambisa a ranar Litinin din da ta gabata.

Ya yi bayanin cewa, sojoji a shirye suke za su tarwatsa wannan kungiya a duk inda suke a wannan gari gudun kada su so sake hadewa, sai dai kuma inji shi, wannan shirin yakar 'yan ta'addan ba yana nufin za'a yi ma garin kawanya ba ne domin ya zama sansanin wannan bata kashi da suke yi tsakanin su da 'yan kungiyar, ganin yadda ake ta yada jita jita na cewa, za'a yi ma garin kawanya, har wassu na shawaratar kowa ya shirya kayan abinci da sauran abin bukata saboda kada a shamace su a hana kowa fita daga gidansa.

Kanar Musa yace dangane da wannan jita jita da ake yadawa ya zama dole ya sanar da jama'a cewa babu gaskiya a cikin wannan labari, don haka kowa ya saki jiki ya yi hidimar gabansa domin babu wani shirin killace garin Maiduguri saboda da fada.

Ya ce kowa ne mutum mai bin doka ya cigaba da yin hidimarsa yadda ya kamata. Abin da rundunar ta saka a gabanta shi ne ganin ta samar da dawwamamnen zaman lafiya da tsaro na rayuka da dukiyoyin jama'a, kuma ana samun wannan nasarar yanzu haka a jihar.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China