A cikin sanarwarsa, shugaba Jonathan ya jaddada cewa, jerin hare-haren da kungiyar Boko Haram ta yi a kwanakin baya ba wai na dan lokaci ne ko laifuffuka kawai ba da ta aikata, sun zama yakin da take yi a zahiri.
Har zuwa yanzu, sojojin gwamnatin Najeriya suna ta farautar dakarun kungiyar Boko Haram. A wadannan yankuna, an rufe dukkan layukan wayar salula da na shafukan intanet, ta yadda za a iya hana dakarun kungiyar da su dauki matakan kai hari ga sojojin gwamnati. Bugu da kari, hukumar soja ta jibge sojoji da yawa a kan iyakar garuruwa da kasashen dake makwabtaka da su, a kokarin hana dakaru masu dauke da makamai na kungiyar tserewa zuwa sauran kasashe.
Watakila aiwatar da dokar ta baci a jihohi 3 dake arewacin kasar Nijeriya zai hana ayyukan dakaru masu tsattsaran ra'ayi a wurin, amma hali rashin zaman lafiya a lokacin bai bayyana cewa za a samu zaman lafiya mai dorewa a dukkan kasar ba.
Ala misali, bisa labarin da hukumar soja ta kasar ta bayar a ranar 17 ga wata, an ce, wasu dakaru sun kai hari ga bankuna da ofisoshin 'yan sanda 4 dake garin Daura a jihar Katsina a ranar 16 ga wata, wadda ke da nisa da yankin da aka kafa dokar ta baci. Wannan hari ya haddasa mutuwar mutane da dama. Don haka, a hakika dai ana fuskantar hali mai tsanani a kusan dukkan kasar Nijeriya, kuma yana da sauki ga dakaru wajen canja sansaninsu a dukkan kasar.
Kafin hakan, kungiyoyin siyasa na kasar Nijeriya sun bada shawara ga shugaban kasar Goodluck Jonathan cewa, kamata ya yi a sanar da aiwatar da dokar ta baci a dukkan kasar Nijeriya, kana sun maida wannan hanya a matsayin shirin karshe na warware matsalar rashin tsaro a kasar. Amma aiwatar da dokar ta baci ba zai iya warware dukkan matsalar rashin tsaro ba. Idan aka yi amfani da karfin soja wajen tsoma baki kan ayyukan kananan gwamnatocin kasar, watakila za a kawo illa ga tsarin siyasa na demokuradiyya na kasar, kana za a zargi wasu kungiyoyin siyasa da suka yi amfani da wannan hanya wajen kawar da sauran kungiyoyin dake da bambancin ra'ayi da su, ta yadda za a kara kawo rikicin siyasa a kasar.
Ban da wannan kuma, yayin da ake daukar matakan yaki da Boko Haram, ana fuskantar da matsalar daidaita dangantakar dake tsakanin murkushe kungiyar ta'addanci da tada rikicin jin kai a kasar.
A kwanakin baya, hukumar soja na kasar Nijeriya ya bada wani umurni a jihohi 3 dake aiwatar da dokar ta baci cewa, za a maida duk wani mutum da ya boye ko ya taimaki 'ya'yan kungiyar Boko Haram a matsayin abokin gaba na gwamnatin kasar. Wannan umurni ya kawo damuwa sosai ga fararen hula dake rayuwa a yankin dake fuskanta rikicin. A cikin watan da ya gabata a garin Baga na jihar Borno, mutane kimanin 200 sun mutu a sakamakon aikin soja da sojojin gwamnatin kasar suka yi, ciki har da mata da kananan yara da dama. A lokacin yaki, abin ne mai wuya wajen tabbatar da tsaron fararen hula. Idan wannan irin lamarin ya sake abkuwa, nasarar da sojojin gwamnatin kasar suka samu ba ta da ma'ana ko kadan ba, kana za a kara tsanantar rikicin jin kai a kasar a nan gaba. (Sanusi+Zainab)