130709-an-samu-babban-cigaba-a-shawarwari-tsakanin-gwamantin-Najeriya-da-Boko-Haram-Murtala
|
Ganin cewa jama'ar musulmi a Najeriya za su fara azumin watan Ramadan, an samu babban ci gaba a wajen shawarwari da aka yi tsakanin kwamitin neman sulhu da daidaitawa tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar nan ta Boko Haram.
Wakilinmu dake Abuja Murtala ya samu damar hira da alhaji Kabiru Tanimu Turaki ta waya, wanda shi ne ministan ayyuka na musamman na kasa, kana shugaban kwamitin sulhu da daidaitawa tsakanin gwamnati da kungiyar Boko Haram, inda ya ba mu karin haske kan wannan batu.