in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Falesdinu
2013-05-06 15:51:47 cri
A ranar 6 ga wata, a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Falesdinu Mahmoud Abbas da ya kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin.

A yayin shawarwarin, shugaba Xi Jinping ya yi maraba da zuwan Abbas a kasar Sin, ya ce, shugaba Abbas ya zama shugaba na farko daga kasashen Larabawa har da na yankin Gabas ta tsakiya gaba daya da ya kawo ziyara a kasar Sin, bayan da aka samu sabuwar gwamnatin kasar, kuma ya yi farin ciki da samun damar haduwa da Abbas, sabo da shi ne wani shahararren dan siyasa a hukumar Falesdinu, kuma ya nace kan bin manufar zaman lafiya, ya samu babban ci gaba wajen shugabancin al'ummar Falesdinawa cikin yunkurin kafa kasar Falesdinu, kuma ya samu goyon baya daga al'ummar Falesdinawa har ma da na kasashen duniya baki daya.

Haka kuma, Mr. Xi ya ce, ya yi imani cewa, a sabon yanayin da ake ciki, ziyarar Abbas a kasar Sin za ta ci gaba da raya dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunta da ke tsakanin kasar Sin da hukumar Falesdinu daga dukkan fannoni, yana fatan yin musayar ra'ayi da Abbas game da raya dangantakar bangarorin biyu, da warware batun Falesdinu, da sauran batutuwan da aka dora muhimmanci sosai a kai.

Shugaba Abbas ya ce, tun daga shekarun 60 na karnin da ya gabata zuwa yau, dangantakar da ke tsakanin Falesdinu da Sin ta dinga habaka, kuma bangarorin biyu sun dau matsayi iri guda game da manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ziyarar da ya kawo a wannan karo ta nuna dankon zumunci da ke tsakanin Falesdinu da kasar Sin.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China