Kasancewar kasar Zimbabwe ta ki amincewa da shigar tawagar masu sa ido ta kasashen yammacin duniya, yawancin masu sa ido daga kasashen waje fiye da 600 da aka yiwa rajista sun fito ne daga kungiyar kawancen raya kasashen kudancin Afirka ta SADC da kuma kungiyar AU. A wannan karo, kungiyar AU ta tura tawagar masu sa ido guda 60 zuwa kasar Zimbabwe, inda 10 daga cikinsu suke kasar tun ranar 15 ga wata domin aikin sa ido ga zaben.
Bisa shirin da aka yi, sauran masu sa ido na kungiyar AU guda 50 za su isa birnin Harare dake kasar ne a karkashin jagorancin tsohon shugaban tarayyar Nijeriya Olusegun Obasanjo a ranar 27 ga wata. Shugaban kasar Robert Mugabe ya yi maraba ga zuwan tawagar.
Ban da kungiyar SADC da ta AU, tsohon wakilin musamman na kasar Sin mai kula da harkokin Afirka Liu Guijin zai jagoranci wata tawagar da za ta isa kasar ta Zimbabwe don aikin na sa ido ga zaben. (Zainab)