Yayin da take zantawa da manema labarai jim kadan da isarta filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Harare, Zuma ta ce, za ta gana da wasu masu ruwa da tsaki yayin ziyarar.
Ta ce, sun zo ne karkashin laimar hukumar kungiyar AU, inda za su tattauna da wasu mutane a wuraren da za a kada kuri'a, hukumar zabe, da 'yan takara don ganin yadda abubuwa ke gudana a zahiri domin ranar zabe.
Ta ce, an yi wa tawagar kungiyar AU mai wakilai 10 da aka turo kasar ta Zimbabwe a ranar 15 ga watan Yuni karin bayani game da irin shirye-shiryen da aka yi dangane da zaben.
Zuma ta kuma bayyana tabbacin cewa, tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo zai zo kasar ta Zimbabwe bayan rahotannin da ke nuna cewa, wata kungiyar da ke kiran kanta da suna Pan African Forum wadda ke karkashin magoya bayan Mugabe ba su gamsu da zuwan nasa ba.(Ibrahim)