Jaridar ta ruwaito Ibrahim Mahmoud Hamid, ministan harkokin cikin gida na kasar Sudan yana fadan haka, inda ya ce sassan biyu sun amince kan shata layin da zai raba da tsarin sa-ido kan wannan mataki, yana mai karawa da cewa,idan aka daidaita bambance-bambancen da ke kasancewa ta bangaren tsaro, hakan zai taimaka wajen magance sauran batutuwa.
A halin da ake ciki kuma, a cewar jaridar, jekadan Sudan ta kudu da ke Addis Ababa Arop Deng, ya sake nanata cewa, sassan biyu sun amince ba tare da gindaya wani sharadi ba na janyewa na nisan kilomita 10 daga yankunan da ake takaddama a kai.
A ranar Litinin ne Sudan da Sudan ta kudu suka koma kan teburin tattauanawa kai tsaye a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha kan batutuwan da har yanzu ba a warware ba karkashin shirin shiga tsakani na AU. (Ibrahim)